Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya amsa wasikar babban darektan WHO
2020-03-26 20:18:16        cri
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya aike masa, inda a cikin ta ya yaba da kokarin da Dr. Tedros ya yi, wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya, kuma a cewarsa, Sin za ta ci gaba da samar wa kasa da kasa tallafi, a kokarin da ake na yakar cutar.

A ranar 17 ga watan nan ne dai Dr. Tedros ya aika wa shugaba Xi Jinping wasika, inda ya ce, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta yi namijin kokarin wajen shawo kan cutar. Sakamakon niyyar gwamnatin kasar, da kuma kokartawar al'ummarta, an dauki matakan da suka dace cikin sauri, kuma daga dukkan fannoni.

Shugaba Xi Jinping a nasa bangaren, ya amsa da cewa, da yake an yi ta samun sassauci a yanayin da ake ciki a kasar Sin, harkokin rayuwa da ayyuka ma suna ta farfadowa, kuma an samu nasara wajen dakile yaduwar cutar, da ma bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na daukar hakikanan matakai, wajen tallafawa kasa da kasa a fannin yaki da cutar, kuma ta samar da gudummawarta ga kungiyoyin duniya, da suka hada da WHO, da ma kasashe sama da 80. Har ila yau kasar Sin za ta ci gaba da samar da tallafinta ga kasa da kasa, gwargwadon karfinta.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, yanayin cutar da ake ciki a duniya ya kara tabbatar da cewa, 'yan Adam makomarsu daya ce, don haka ya kamata kasa da kasa su zama tsintsiya madaurinki guda, wajen tinkarar cutar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China