Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana son zurfafa muamalar dake tsakaninta da kasashen Afirka da Turai da Asiya kan aikin yakar cutar COVID-19
2020-03-19 19:56:01        cri

Yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya yi bayani kan yadda kasar Sin take gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, Turai da Asiya wajen yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Yayin taron manema labaran da aka kira a yau, Geng Shuang ya ce, jiya Laraba, kasar Sin da kasashen Afirka sun yi taron kwararru ta kafar bidiyo kan yadda za a yi aikin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Jami'ai da kwararru kimanin 300 na kasashen Afirka da suka halarci wannan taro, sun nuna yabo matuka kan babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da cutar, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye tsaron lafiyar al'ummar kasa da kasa. Sun kara da cewa, taron ya zo a lokacin da ya dace, kuma sun amfana kwarai da gaske.

Bugu da kari, Geng Shuang ya ce, da yammacin gobe Jumma'a, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, hukumar kiwon lafiya da hukumar kwastam ta kasar Sin, za su shirya taron karawa juna sani kan matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da wasu kasashen dake yankin Asiya da Turai da kudancin Asiya sama da guda 10.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana son ba da karin gudummawa wajen tunkarar kalubalen lafiyar al'umma da duniya ke fuskanta, da kare muradun bil-Adama ta hanyar kungiyoyi kamar G20. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China