Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin mutane 55 da suka kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin Sin
2020-03-27 09:37:35        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Jumma'a cewa, ta samu sabbin mutane 55 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin a ranar Alhamis, kana 54 daga cikin adadin an shigo da su ne daga ketare.

A cewar hukumar, a ranar Alhamis din, an samu mutuwar mutane 5 da kuma wasu 49 da ake kyautata zaton sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin, yayin da dukkan wadanda suka mutu a wannan rana a lardin Hubei ne.

A wannan rana ta Alhamis, an sallami mutane 537 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, yayin da adadin mutanen dake cikin tsananin cutar ya ragu da mutane 201 inda ya koma mutane 1,034. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China