Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara fahimtar kwayoyin cutar numfashi ta COVID-19
2020-03-20 20:36:15        cri
Wasu suna damuwa cewa, ko kayayyakin kirar Sin suna dauke da cutar numfashi ta COVID-19? Game da wannan batu, binciken da muka yi ya nuna mana cewa, bai kamata jama'a su nuna damuwa kan wannan jita-jita maras tushe ba!

Da farko, kasar Sin ta gaggauta daukar matakan hana yaduwar cutar yadda ya kamata, ta killace dukkanin masu kamu da cutar da ma wadanda ake zaton suna dauke da cutar, lamarin da ya tabbatar da cewa, wadanda suka kamu da cutar ba za su iya shiga cikin masana'antu ba.

Sa'an nan kuma, kwayoyin cutar ba za su iya rayuwa na dogon lokaci ba. Bincike ya nuna cewa, tsawon lokacin da kwayoyin cuta za su iya rayuwa a kan karfe ba zai wuce awo'i biyu ba, da kwanaki 2 a kan gilashi da kuma kwanaki 9 a kan roba.

Ban da haka kuma, kwayoyin cutar suna dogaro kan kwayar halittu, in babu kwayar hallita da za su iya dogaro a kai, ba za su iya rayuwa ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China