Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sanar da ba da taimako ga kasashe 82
2020-03-20 20:59:02        cri
Yau Jumma'a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta manta goyon baya da taimakon da gamayyar kasa da kasa suka ba ta a lokacin da take cikin mawuyacin hali na fama da cutar numfashi ta COVID-19 ba. Kuma a halin yanzu, kasar Sin ta taimakawa kasashen dake fama da cutar. Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta sanar da ba da taimako ga kasashe guda 82, da hukumar lafiya duniya ta WHO da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU.

Haka kuma, ya ce, munanan kalaman da kasar Amurka ta yi kan martanin da kasar Sin ta mayar mata kan yadda take musugunawa kafofin watsa labaranta dake Amurka, ya nuna fuska biyu na kasar Amurka. Kasar Sin tana fatan kasar Amurka za ta yi tunani kan kuskuren da ta yi, da kuma daina bata sunan Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da ma kafofin watsa labaran kasar Sin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China