Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: Cutar COVID-19 ba za ta karya tattalin arzikin Sin ba
2020-03-20 19:11:53        cri
Jiya Alhamis, shehu malami a fannin siyasa da dangantaka tsakanin kasa da kasa na jami'ar Abuja, Sheriff Ibrahim ya rubuta wani sharhi a jaridar Blueprint mai taken "Tattalin arzikin Sin na farfadowa, bisa nasarar da ta cimma wajen yaki da cutar COVID-19", inda ya nuna yabo ga al'ummar Sinawa kan yadda suka hada kai a lokacin yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce, al'ummar Sinawa sun cimma muhimmin sakamako bisa babbar aniyar da suka nuna.

Sharhin ya ce, kasar Sin tana da tsarin tattalin arziki mai karfi, da masana'antu a fannoni daban daban, kuma al'ummomin kasar suna da kwarin gwiwa, lamarin da ya sa kasar ta iya farfado da ayyuka cikin sauri. Kuma tabbas, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin za ta samar da damammaki ga bunkasuwar kasa da kasa, da kawar da tasirin da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China