Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Masisi na Botswana ya kebe kansa bayan ya ziyarci kasar Namibia
2020-03-23 09:30:35        cri
Shugaban kasar Botswana, Mokweetsi Masisi, ya fara kebe kansa na tsawon kwanaki 14, daga ranar Asabar, 21 ga wata, biyo bayan ziyarar da ya kai kasar Namibia.

Wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar a jiya, ta ce hikimar daukar wannan mataki shi ne, yayin da Namibia ke da mutane 3 masu dauke da cutar, wadanda suka shiga kasar da ita, ana ganin hadarin yaduwar cutar a kasar ba shi da yawa a lokacin da shugaban na Botswana ya kai ziyara, sai dai rashin karfin gwaji a yankin ya sa samun tabbacin hakan zai yi wuya.

Sanarwar ta ce, yayin zaman na kebe kai, za a gwada shugaba Masisi don tabbatar da ko ya kamu da cutar ko a'a. Sannan zai ci gaba da aiki daga gida, amma kuma nesa da iyalinsa ba.

Darakta mai kula da batun cutar COVID-19 a ma'aikatar lafiya ta kasar, Malaki Tshipayagae, ya nemi sauran ma'aikatan da suka yi tafiya tare da shugaban, su ma su kebe kansu.

Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa, Shugaba Masisi ya yi tafiyar gaggawa zuwa Namibia ne a ranar Asabar, domin samun damar ganawa da sauran shugabannin yankin da suka hadu a birnin Windhoek na kasar, domin tattauna matakan da ya kamata a dauka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, a kasashen dake iyaka da Botswana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China