Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta dakatar da baki daga ketare masu takardun visan zama da shiga kasar zuwa wani lokaci
2020-03-27 11:35:21        cri

A jiya ne ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da hukumar kula da shige da fice sun sanar da dakatar da baki daga ketare dake da visa ko takardar shaidar zama a kasar shiga kasar zuwa wani lokaci.

Sanarwar ta ce, kasar Sin ta dauki wanan mataki ne, ganin yadda cutar COVID 19 ke kara yaduwa a duniya, wanda zai fara aiki da karfe 12 na tsakar daren yau Jumma'a. Amma, wannan mataki ba zai shafi ma'aikatan diflomasiya da manyan jami'an gwamnatin sauran kasashe da aka gayyata da masu rike da visa rukunin C. Sanarwar ta ce, baki da dole sai sun shigo kasar Sin don gudanar da harkokin cinikayya, kimiyya da fasaha ko aikin jin kai na gaggawa, za su iya neman visa a ofisoshin jakadancin Sin dake ketare. Haka kuma, ba za ta shafi wadanda suka samu visa bayan wannan sanarwa ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China