Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CGTN zai gabatar da shirin tattauna fasahohin jinyar gargajiyar Sin
2020-03-26 13:55:13        cri

Yau da misalin karfe 8 da dare ne, gidan talabijin kasa da kasa na kasar Sin wato CGTN na babban gidan rediyo da talabijin kasar Sin wato CMG zai gabatar da shirin talabijin na "dandalin jinyar cutar numfashi ta COVID-19 na kasa da kasa", taken shirin na wannan karo shi ne tattauna fasahohin jinyar gargajiyar kasar Sin, inda masana fasahohin jinyar gargajiyar kasar Sin za su yi mu'amala da likitocin kasashen ketare ta kafar bidiyo, kan yadda fasahohin jinyar gargajiyar Sin suka ba da gudummawa wajen samar da jinya ga wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma fasahohin da suka koya a yaki da cutar COVID-19.

Ya zuwa ranar 24 ga wata, adadin mutanen da suka kalli shirye-shiryen "dandalin jinyar cutar numfashi ta COVID-19 na kasa da kasa" da CGTN ya watsa a duniya ya kai miliyan 33 da dubu 150, yayin da adadin wadanda suka kalli bidiyon ya kai miliyan 9.23, sa'an nan, mutane sama da dubu 130 sun bayyana ra'ayoyin su kan shirin ta yanar gizo. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China