Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalibai a sassan Sin za su koma makarantu
2020-03-26 13:06:38        cri

Sakamakon kyautatuwar yanayi da aka samu ta fuskar dakile cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, sassa daban daban na kasar suna shirin bude makarantu, domin dawo da harkokin karatu.

Daliban aji 3 na makarantun sakandare sama da dubu 250 a lardin Shanxi dake tsakiyar kasar sun koma makarantu a ranar 25 ga wata, adadin da ya kai 99% na dukkanin daliban dake aji 3 a wannan lardi. Kuma dukkanin makarantun lardin sun dauki matakan kandagarki da suka hada da auna zafin jikin dalibai a kofofin shiga makarantu, rage adadin daliban dake karatu cikin aji guda, da raba lokacin cin abinci da dai sauransu.

Haka kuma, hukumar ilmi ta lardin Sichuan ta bayyana cewa, dalibai da malamai za su iya komawa karantu bisa tushen kare lafiyarsu.

A birnin Shenyang na lardin Liaoning, gwamnatin ta sanar da cewa, in babu isassun kayayyakin kandagarki, ba za a yarda dalibai su dawo makarantunsu ba. Yanzu kuma, birnin Shenyang ya riga ya tura likitoci guda 405 daga cibiyoyin ba da hidimar kiwon lafiya a unguwanni da asibitoci zuwa makarantu guda 350 da ba su da isassun likitoci, kuma dukkansu sun fara aiki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China