Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tabbatar da karin mutane 67 da suka kamu da cutar COVID-19
2020-03-26 13:05:59        cri

Alkaluman kididdigar da hukumar lafiya ta kasar Sin ta fitar na cewa, a jiya Laraba, ta samu rahoton karin mutane 67 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar, kuma dukkansu sun shigo da cutar ce daga ketare. Haka kuma karin mutane 6 sun mutu a sakamakon cutar. Kana karin mutane 58 da ake zaton sun kamu da cutar, dukkan su sun shigo da cutar ce daga ketare. Ya zuwa jiya Laraba yawan wadanda suka shigo da cutar daga ketare ya kai 541.

Haka kuma ya zuwa jiyan, jimilar wadanda suka kamu da cutar ta kai 81285, yayin da ake zaton wasu 159 da kamuwa da cutar a babban yankin kasar. Haka kuma mutane 74051 sun warke daga cutar, an kuma sallame su daga asibiti, kana mutane 3287 sun rasa rayukansu sanadiyar cutar.

Kana ya zuwa jiyan, jimilar mutanen da suka kamu da cutar a yankin Hong Kong da Macau da Taiwan na kasar Sin ya kai 675. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China