Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce Sin a shirye take ta bunkasa hadin gwiwa da kasa da kasa don yakar COVID-19
2020-03-26 10:08:05        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin daukar matakan dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 tare da nuna kwarin gwiwar yin galaba kan cutar a matakan kasa da kasa.

Xi ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, gabaninn taron kolin shugabannin kasashen G20 dake tafe wanda za'a gudnaar ta hanyar bidiyo wanda zai mayar da hankali kan matakan tinkarar annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Shugaba Xi ya ce, kasar Jamus tana fuskantar mummunan kalubale game da yaduwar annobar a halin yanzu, haka su ma al'ummar kasar Sin suna cikin halin damuwa game da annobar da ta barke, ya kara da cewa, kasar Sin ta sha alwashin taimakawa Jamus don yaki da cutar kuma a shirye take ta ci gaba da tallafawa kasar gwargwadon ikonta.

Kwayoyin cutar ba sa la'akari da kan iyakoki kuma matsala ce da ta shafi dukkan bil adama, in ji shugaba Xi, ya kara da cewa, babu wata kasa a duniya da za ta iya tsame kanta daga annoba.

A yayin da ake shirin gudanar da taron kolin na G20, Xi ya ce, bangaren kasar Sin a shirye yake ya yi aiki tare da dukkan bangarori na duniya ciki har da kasar Jamus, domin daukar matakai tare da yin magana da murya daya don yin musayar kwarewa da hada hannu wajen yakar annobar cutar numfashi ta COVID-19, domin samun gwarin gwiwar ceto al'ummar kasa da kasa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China