Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta raba fasahohinta na kimiyya da fasahohi ga kasashen duniya
2020-03-26 13:45:30        cri

Mataimakin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Nanping ya bayyana a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a yau cewa, tun lokacin da cutar COVID-19 ta barke, Sin ta raba fasahohinta na kimiyya da fasahohi da dabarun yaki da cutar ga bangaren kimiyya da fasaha na duniya. Hadin gwiwa don tinkarar cutar tare ya zama muhimmin aiki yayin da Sin take amfani da daharu na kimiya da bincike wajen yaki da cutar

Ban da wannan kuma, mataimakin shugaban hukumar kula da hadin gwiwa da bunkasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin Deng Boqing ya bayyana a yayin taron cewa, hukumomin gwamnatin kasar Sin da kamfanonin da abin ya shafa na kasar sun gudanar da ayyukan bada gudummawa ga kasashen waje. A halin yanzu, kasar Sin ta tsara tare da samar da taimako karo na 4 wajen yaki da cutar ga kasashe 89 da kungiyoyin kasa da kasa guda 4, kana yanzu tana kokarin tsara shirin ba da taimako karo na biyar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China