Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An farfado da layoyin zirga-zirgar jama'a sama da 100 a birnin Wuhan
2020-03-25 13:06:25        cri
Daga yau Laraba 25 ga wata, za a dawo da hanyoyin motocin zirga-zirgar jama'a guda 117 a birnin Wuhan, domin warware matsalar zirga-zirga ga wadanda suka dawo bakin ayyukansu a birnin Wuhan na lardin Hubei dake zaune a sauran larduna. Sa'an nan, daga ranar 28 ga wata, za a dawo da layukan jiragen kasan cikin birni guda shida.

Kwanan baya, hukumar kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta lardin Hubei ta fidda sanarwa game da haramcin tafi daga lardin Wuhan, da shirin dawo da ayyuka a birnin Wuhan, inda ta bayyana cewa, mutanen dake zaune a sauran larduna za su iya shiga birnin Wuhan da ma sauran wuraren lardin Hubei, bisa shaidar lafiya da lardunansu suka ba su, ko kuma shaidar lafiya da lardin Hubei ya ba su. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China