Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an MDD sun nuna damuwa kan yadda ake nunawa wasu tsangwama da sunan COVID-19
2020-03-27 10:08:14        cri
Babban wakilin kawancen MDD kan wayewar kai Miguel Moratinos da mai baiwa babban sakataren MDD shawara na musamman kan yaki da kisan kiyashi Adama Dieng, sun nuna matukar damuwarsu kan yadda ake kara samun kalaman nuna kiyayya da tsangwama kan daidaikun mutane da kungiyoyi babu gaira babu dalili da ake ganin suna da nasaba da cutar COVID-19

Jami'an sun bayyana haka ne, cikin wata sanarwar hadin gwiwa, suna masu cewa, annoba, babban makiyin daukacin bil-Adam ne, kuma babu wanda yake ganinta, tana kuma ci gaba da bazuwa kamar wutar daji, da ma lakume rayukan jama'a da haddasa barna ba sani ba sabo. Amma, idan har muka bari, wannan matsala ta raba kan al'ummominmu, da alamun wannan na iya zama bala'i mafi muni da annobar COVID-19 din za ta haifarwa duniyarmu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China