Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar Johns Hopkins: Amurka ta zama kasa mafi yawan masu dauke da cutar COVID-19
2020-03-27 10:09:47        cri
Cibiyar nazarin tsarukan kimiyya da aikin injiniya ta Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta ce ya zuwa jiya Alhamis karfe 6 na yamma agogon gabashin kasar, akwai jimilar mutane 82,404 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar.

A cewar cibiyar, Amurka har ta zarce kasar Sin, inda ta zama kasar da ta fi ko wacce yawan wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya.

Adadin masu cutar a kasar ya karu ne, bayan sama da mutane 10,000 sun kamu cikin kasa da sa'o'i 5. Jihar New York dake da masu dauke da cutar 37,802, ta zama wurin da cutar ta fi kamari. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China