Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da bullar cutar COVID-19 a kasashen Ghana da Gabon
2020-03-13 10:52:27        cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Ghana ta sanar a jiya Alhamis cewa, a karon farko an tabbatar da rahoton mutane biyu da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta bayyana cewa, marasa lafiyan guda biyu, sun dawo kasar ta Ghana ce daga Norway da Turkiya.

A wani labarin kuma, ministan sadarwa kana kakakin gwamnatin kasar Gabon Edward Anicet Mboumbou Miyakou, ya sanar ta gidan talabijin na kasar a jiya Alhamis cewa, mahukuntan kasar sun tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar COVID-19. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China