Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu sabon wanda ya kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-03-25 10:17:06        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Laraba cewa, ba ta samu rahoton wani da ya kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar ba a jiya Talata.

Sai dai, hukumar ta ce ta karbi rahoton sabbin mutane 47 da aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin a jiyan, tana mai cewa dukkansu shigo da cutar suka yi daga ketare.

Har ila yau a jiya, mutane 4 sun mutu inda ake zaton wasu sabbin mutane 33 sun kamu a babban yankin kasar. An samu dukkan mace-macen ne a lardin Hubei. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China