Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CGTN ya gabatar da shiri mai taken "Dakin ba da jiyya na kasa da kasa kan COVID-19"
2020-03-24 14:23:49        cri

Kwanan baya, gidan telibijin na kasa da kasa CGTN dake karkashin jagorancin babban rukunin gidan rediyo da telibiji na kasar Sin CMG, ya gabatar da wani shiri na musamman mai taken "Dakin ba da jiyya na kasa da kasa kan COVID-19", inda aka kira wani taro ta bidiyo tsakanin wasu likitoci masu taimakawa birnin Wuhan daga asibitin Peking Union Medical College da likitoci daga cibiyar ba da jinyya ta Princeton ta kasar Amurka, inda suka tattauna kan manufofin magance cutar da kuma dabarun rage damuwa da fargaba da masu jinyya ke yi da dai makamatansu.

Wannan shiri na musamman da CGTN ya gabatar na kokarin taimakawa tinkarar cutar, ya gayyaci masu aikin jinyya dake aiki a wuraren da cutar ta fi kamari a duniya, inda ya kasance wani dandali da masana suka yi musayar ra'ayi kan fasahohi da dabarunsu na yaki da cutar ta kafar bidiyo. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka kalli wannan shiri a kan intanet ya kai miliyan 33.15, kuma yawan mutane da suka kalli wannan bidiyo ya kai miliyan 9.23, mutanen da suka yi musanyar ra'ayi game da wannan shiri sun kai dubu 130. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China