Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ba ta da niyyar haramta tafiye-tafiye saboda cutar COVID-19
2020-03-13 09:26:25        cri
Ministan lafiya na Nijeriya Osagie Ehanire, ya ce gwamnatin kasar ba ta da niyyar haramta shiga kasar ga matafiya daga kasashen ketare, saboda yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Ministan wanda ya bayyana haka jiya yayin wani taro da jami'an diflomasiyyar kasashen waje a Abuja, babban birnin kasar, ya ce matakan da gwamnatin ta dauka na da karfin tunkarar yaduwar cutar.

Ya kara da cewa, a yanzu dai, babu wani dalili na hana shiga kasar.

Har ila yau, ya ce kasar ba ta kai matakin hana gudanar da manyan taruka ba, yana mai cewa tana kiyaye ka'idojin hukumar lafiya ta duniya WHO. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China