Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira ga kasashen Afirka da su hada kai don dakile COVID-19 a nahiyar baki daya
2020-03-13 09:59:03        cri
Kungiyar tarayyar Afirka wato AU a takaice, ta jaddada muhimmancin hada kai don daukar matakai na bai daya, don dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar baki daya.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU mai mambobin kasashe 55 ne ya yi wannan kiran, cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis, bayan wani taro da kungiyar ta kira, wanda ya mayar da hankali kan barkewar cutar COVID-19 a nahiyar Afirka.

Bugu da kari, kwamitin ya shawarci daukacin kasashen Afirka, da su karfafa matakansu na gwajin cutar, da kara inganta kayayyakin kiwon lafiyarsu baki daya.

Taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar na zuwa ne, kwana guda bayan da a ranar Laraba hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya, yayin da kwayar cutar ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Afirka(CDC) hukumar kungiyar AU da ta kware a fannin kula da kiwon lafiya, ta bayyana cewa, sama da mutane 100 sun harbu da cutar a kasashe 12 na Afirka, ciki har da Aljeriya da Burkina-Faso da Kamaru, da Cote d'Ivoire,da Jamhuriyar demokiradiyyar Congo, da Masar, da Morocco, da Najeriya. Sauran sun hada da Senegal, da Afirka ta kudu, da Togo da kasar Tunisiya.

CDC wadda ta sanar da canja shirin tunkarar cutar zuwa kandagarki, ta ce a halin yanzu, kwamitin nahiyar na musamman kan tunkarar cutar(AFTCOR) yana taimakawa matakan kasashen nahiyar na dakile cutar, inda yanzu haka kasashen nahiyar 43, tare da taimakon CDC da WHO suna da karfin gwajin kwayar cutar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China