Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lawal Saleh: Kokarin gwamnatin kasar Sin na dakile COVID-19
2020-03-13 10:07:09        cri

Masanin harkokin kasa da kasa dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, malam Lawal Saleh ya rubuta wani sharhi mai taken "Kokarin Gwamnatin Kasar Sin Na Dakile COVID-19".

Lawal Saleh ya ce, kasar Sin ko kuma Jamhuriyar Jama'ar Sin kasa ce mai bin ra'ayi irin na kwaminisanci da kuma tsarin gurguzu. A shekarar 1949 aka kaddamar da ita a tafarkin Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin wato PRC. Tun wannan lokacin ne, kasar Sin ta shiga tsari irin na hada kan al'umma da kuma taimaka ma 'yan kasa a fannoni daban-daban kamar su harkar noma, da kiwon lafiya, da sama wa 'yan kasa aikin yi da tanadar da muhalli.

Ba abin mamaki ba ne a yayin da kasar ta samu kanta a mawuyacin hali na cutar numfashi wato COVID-19 a Wuhan a cikin lardin Hubei na tsakiyar kasar, aka ga hobbasa da yunkurin gaggawa wanda shugaba Xi Jinping ya bada umurni. Shugaba Xi Jinping dai shi ne sakatare janar na jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma jagoran dakarun sojan kasar. A tun lokacin da cutar COVID-19 ta bulla a Wuhan na cikin lardin Hubei a watan Disamba na bara 2019, masu mulkin kasar Sin sun dauki matakai daban-daban domin ganin an dakile cutar a cikin gaggawa.

Matakan da aka dauka dai masu burgewa ne da jinjinawa a yayin da ma'aikatan jinya, da sojoji, da 'yan sanda da masu aiki a kananan hukumomi, da masu noman abinci, da 'yan aika-aika da dai sauransu duk suka kawo dauki a Wuhan domin ganin an yaki wannan cuta ta COVID-19.

Killace garin Wuhan da aka yi a yayin da ba shiga ba fita ba karamin tasiri ya yi ba saboda ya hana yaduwar cutar matuka zuwa ga sauran larduna da garuruwan kasar da kuma kasashen waje ma. A ci gaba da kokarin baiwa mutanen da cutar ta COVID-19 ta shafa a garin na Wuhan, gwamnati a karkashin shugaba Xi ta yi alkawarin gina asibitoci cikin kwana goma kuma ta cika alkawari, a yayin da aka gina asibitoci na Leisheshan da Huoshenshan masu gado akalla dubu uku. Bayan wannan kokarin ma an mayar da filayen wasanni da dama zuwa asibitocin wucin gadi domin kulawa da majiyyata.

Wani abin sha'awa wanda kasashen duniya ya kamata su yi koyi da shi shi ne yadda likitoci da nas-nas da 'yan agaji suka sadaukar da kansu a wajen aiki tukuru domin kulawa da masu fama da ciwon numfashi na COVID-19. Kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ita ma ta jinjina ma kasar Sin tare da shuwagabannin kasar a kokarin dakile wanan cuta. Bayan haka ma kasashe da dama a ciki har da Nijeriya duk sun nuna jin kai da kuma goyon baya da addu'o'i ma kasar Sin domin ganin an ci nasara a kan cutar COVID-19.

Irin matakan da kasar Sin ta dauka dai suna daga cikin tsare-tsare irin na gurguzu a yayin da gwamnati take tausaya wa duk dan kasa da ya shiga mawuyacin hali. Shugaba Xi Jinping tare da da firimiya Li Keqiang da jigogin jam'iyyar kwaminis duk sun tashi tsaye a kan ganin an ci nasara a kan cutar COVID-19 har karshe. A sakamakon haka ne ma kullum ake samun raguwar masu kamuwa da kuma karuwar masu warkewa da cutar. Rahotanni sun nuna cewa a halin da ake ciki, dubban marasa lafiya sun warke kuma an sallame su daga asibiti. Haka kuma an rufe asibitoci sama da talatin dangane da raguwar sabbin majiyyata.

A kokarinsa na baiwa ma'aikatan kiwon lafiya da tausaya ma mutanen Wuhan da cutar ta shafa, shugaba Xi Jinping ya yi rawar gani a yayin da ya yi tattaki ya ziyarci garin Wuhan a ranar 10 ga wata domin gani da idonsa da kuma jinjina musu, inda ya ce: "Tare da kakkarfar manufa, mutanen Wuhan sun nuna karfin zuciya irin na kasar Sin da kuma nuna soyayyar 'yan uwa da kasa baki daya wacce ta hada kan Sinawa a kowane halin da suka samu kansu". A yayin da ya ziyarci asibitin Huoshenshan, ya bayyana matukar farin cikinsa a yanda masu aikin jinya suka sadukar da rayuwarsu domin ceton al'umma.

Bayan shugaba Xi ya bar asibitin Huoshenshan dai ya garzaya zuwa sabon garin Donghu a inda ya nemi sanin kokarin da mutanen garin suka yi na samun nasara a kan yakin da suka yi da wannan cuta ta numfashi wato COVID-19.

Ya zuwa yanzu dai mutanen da suka samu saukin wannan cuta kuma suka warke suna ta komawa gidjensu, likitoci ma suna cire kayan da suka sa na musamman. Harkokin yau da kullum ma suna dawowa kamar yanda aka saba. Cutar dai ta COVID-19 kamar yanda aka sani ta fi yawa a Wuhan na lardin Hubei a inda kashi kusan 80% na duk wanda suka kamu suna a Wuhan da wasu garuruwa a cikin lardin Hubei.

A ci gaba da taimaka wa al'ummar kasar Sin a tsarin irin na gurguzu mai akida ta Sin, ana ci gaba da yaki da talauci tukuru. Shugaba Xi Jinping dai ya jaddada manufarsa ta fatattakar talauci a inda ya ce: "A yayin da aka gama fatattakar talauci cikin shekarar 2020, kasar Sin za ta cimma nasarar ajanda ta 2030 ta Majalisar Dinkin Duniya shekara goma kafin lokacin da aka kiyasta". Shugaba Xi ya ci gaba da cewa: "Wannan dai babban tasiri ne ga kasar Sin da kuma duniya baki daya". Kasar Sin dai ta yi rawar gani a kan yaki da talauci a yayin da ta fitar da mutane kusan biliyan daya daga kangin talauci. (Lawal Saleh, masanin harkokin kasa da kasa dake Abuja, Najeriya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China