Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin WHO Ya Yi Bayani Kan Ko Kasar Sin Ta Taba Boye Rahoto Kan Cutar COVID-19 Ko A'a
2020-03-19 21:03:17        cri

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaran kasar Amurka sun yi zargin cewa, da gangan kasar Sin ta boye rahoton bullar cutar numfashi ta COVID-19, ta mayar da kasashen duniya baya wajen yaki da cutar, da kuma haddasa matsala da ma hasara ga sauran kasashen duniya, domin boye rashin karfinsu na dakile yaduwar cutar, da kuma amfani da wannan annoba wajen bata sunan kasar Sin.

A hakika, bayan barkewar cutar, kasar Sin ta gabatar da labaran da abin ya shafa ga kasa da kasa nan take, kuma ba tare da boye kome ba, domin kiyaye tsaron lafiyar al'ummar kasa da kasa, ta kuma dukufa wajen yin hadin gwiwa da kasashen duniya domin dakile yaduwar cutar. Kuma bisa kokarin da kasar Sin ta yi, ta cimma nasarar hana yaduwar cutar cikin wata guda daya. A ranar 18 ga watan da muke ciki yanzu, ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar a lardin Hubei ba, lamarin da ya nuna kyakkyawan yanayin da kasar Sin take ciki wajen dakile yaduwar cutar.

Kokarin da kasar Sin ta yi ya kasance muhimmin mataki na farko ga gamayyar kasa da kasa wajen hana yaduwar cutar, Sin ta kuma samu yabo matuka daga gamayyar kasa da kasa. Kwanan baya, wakilin hukumar WHO dake kasar Sin Gauden Galea ya yi bayani kan wasu batutuwan da kasar Sin ta yi domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Ya ce, ofishin hukumar WHO dake kasar Sin ya samu sanarwa kan cutar daga gwamnatin kasar Sin a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar da ta wuce. Sa'an nan, A ranar 1 ga watan Janairu kuma, hukumar WHO ta kira taro a ofishinta dake kasar Sin da ofisoshin yankin da hedkwatar hukumar dake birnin Geneva ta wayar tarho, inda kuma ta kafa tawagar fuskantar da matsalar kafin ranar 3 ga watan Janairu, watau lokacin da kasar Sin ta gabatar da batun a hukumance. Sa'an nan, a ranar 20 da 21 ga watan Janairu kuma, wakilan ofishin hukumar dake kasar Sin sun kai ziyara a birnin Wuhan.

Bugu da kari, ya ce, wannan bayani ya kawar da ikirarin da ake cewar, wai kasar Sin ta boye bayanai kan cutar. A hakika, dalilin da ya sa, hukumar ta iya nazari kan yanayin cutar yadda ya kamata sabo da bayanin da kasar Sin ta gabatar mata cikin sauri, lamarin da ya ba da babbar gudummawa ga gamayyar kasa da kasa wajen tsara shirin yaki da cutar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China