Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nuna rashin jin dadi ga matakan magance cutar COVID-19 na Amurka
2020-03-17 16:39:31        cri
Jiya Litinin 16 ga wata, alkaluman "the Dow Jones Industrial Average" wato DJIA, sun fadi da kusan kaso 13 bisa dari, faduwar da ita ce mafi muni cikin shekaru 30.

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka, ya bayyana a yayin taron manema labaru a fadar gwamnati wato White House cewa, kila tattalin arzikin kasar zai samu koma-baya. Wannan shi ne karo na farko da ya ambato illolin da annobar za ta haifar. Amma shugaba Trump ya nuna gamsuwa sosai ga matakan da ya dauka wajen tinkarar cutar.

Cibiyar nazarin harkokin Sin da duniya a zamanin yau na hukumar wallafa litattafan harsunan waje ta kasar Sin ta yi nazari kan labaru kimanin dubu 200, da manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar tun daga ranar 20 ga watan Janairu zuwa ranar 13 ga watan Maris.

Manyan batutuwan uku da jama'a suka fi sa lura, su ne hanyoyin da aka kidaya yawan mutanen da suka kamu da cutar, da damuwa da yaduwar cutar a unguwoyi, da kuma kara samun matsala, idan aka dauki matakai marasa amfani.

An shaida cewa, yawancin zargin da aka yi wa gwamnatin kasar Amurka su ne kasa kula da tsananin bazuwar annobar, da kasa jagorancin jama'a wajen yakar annobar, da kuma daukar matakan magance cutar ba a kan lokaci ba.

Abin mamaki shi ne bisa wannan yanayi, shugaba Trump bai gano kuskuren sa ba, kuma ya kara bayar da jita-jita, da ci gaba da zargin kasar Sin. A daren ranar 16 ga wata, ya bayyana a kan Twitter cewa, kasar Amurka za ta nuna goyon baya ga sana'o'in da kwayoyin cutar kasar Sin suka kawo illa.

Kafin hakan, direktan cibiyar kula da cututtuka ta kasar Amurka Dr Redfield ya amince da cewa, tun daga ranar 29 ga watan Satumba na bara, wasu mutanen da suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar mura iri ta Flu da ta haddasa mutuwar mutanen Amurka fiye da dubu 20, mai yiwuwa ne sun kamu da cutar COVID-19.

Don haka, zargin shugaba Trump ya jawo kin amincewa daga masu amfani da yanar gizo. Wani likitan kasar Amurka mai asalin kasar Sin ya bayyana a kan Twitter cewa, Trump ya maida matakan magance cutar a matsayin ra'ayin nuna kyamar baki, da kiran COVID-19 da sunan kwayoyin cutar kasar Sin. Shugaban kasar Amurka ya zabi wannan hanya maras haske, don haka kasar mu za ta kara tinkarar matsaloli.

Yayin da ake tinkarar kalubalen duniya, ya kamata kasa da kasa su daina kin zargin juna, su yi hadin gwiwa don cimma nasarar yaki da cutar a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China