Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ke iya daukar managartan matakan dakile annobar COVID-19 amma wasu kasashe suka gaza ?
2020-03-07 16:55:10        cri
Bruce Aylward, babban mashawarcin darakta janar na hukumar WHO, ya zanta da jaridar New York Times ta kasar Amurka a baya bayan nan, inda ya bayyana yadda yake gudanar da bincike kan annobar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kwanaki 9 a kasar Sin, da jinjinawa managartan matakan da gwamnatin kasar ke dauka domin hana yaduwar cutar, ciki har da killace jama'a a gida, da rufe birane da kuma makarantu daban daban.

Sai dai, dan jaridan New York Times ya yi tsokaci cewa, "ba zai yiwu a dauki irin wadannan matakai a Amurka ba", kana "dalilin da ya sa kasar Sin ta yi hakan shi ne, ita kasa ce mai kama-karya".

 

Irin furucin dan jaridar New York Times, ya bata nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin dakile yaduwar cutar, kana ya nuna bambanci da rashin sani da wasu 'yan kasar Amurka ke da shi. Abun da ba su fahimta ba shi ne, duba da irin managarcin tsarin da kasar Sin ke tafiyarwa, kasar tana hada kan daukacin al'ummominta wajen daukar matakan dakile cutar ba tare da wani jinkiri ba, wadanda ba kiyaye lafiyar jama'ar kasar kadai suka yi ba, har ma da taimakawa ayyukan ganin bayan annobar a fadin duniya.

 

 

Abun lura shi ne, Amurka na da matsaloli da dama yayin da take gudanar da ayyukanta na hana yaduwar cutar COVID-19, ciki har da rashin gudanar da bincike cikin sauri, da bukatar kashe kudade masu yawa domin samun magani, inda har manyan jam'iyyun siyasar kasar ke ce-ce-ku-ce game da batun samun tallafin kudi don yakar annobar. Kana, ba zato ba tsammani, cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar, ta sanar da dakatar da bayyana adadin mutanen da ta yi bincike kansu, duk da ana samun karuwar yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar.

 

 

Tambayar a nan ita ce, mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ke iya daukar managartan matakai masu karfi don ganin bayan annobar, amma ita kasar Amurka ta kasa? Amsar ita ce, bambanci tsakanin shugabanci nagari da akasinsa, da kuma bambanci tsakanin babbar kasa mai sauke nauyi dake wuyanta da wadda ta mayar da muradunta sama da komai.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China