Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping na jagorantar al'ummar kasar Sin wajen samun nasarar dakile annobar COVID-19
2020-03-07 20:51:16        cri
Annobar cutar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya a halin yanzu, amma a nan kasar Sin, adadin sabbin mutanen da suka kamu da cutar gami da wadanda suka mutu sakamakon cutar duk suna ta raguwa cikin sauri, kana, tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar kasar na farfadowa.

A matsayin shugaban kasar Sin, Xi Jinping yana nuna himma da kwazo wajen jagorantar daukacin al'ummar kasarsa don ganin bayan cutar.

 

 

Tun bayan barkewar annobar, ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba Xi ya jagoranci muhimman taruka da dama, domin tsara manufofin yaki da cutar. Har wa yau, sau da dama ya yi ziyarar gani-da-ido zuwa birane da garuruwa da kuma cibiyoyin binciken dabarun yaki da cutar. Al'ummar sassa daban-daban na kasar ma sun tashi tsaye bisa umarnin shugaba Xi, a wani kokari na tabbatar da ayyukan kandagarkin yaduwar cutar da na raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma. Hakan ya sa kwalliya ke biyan kudin sabulu wajen ganin bayan yaduwar cutar a kasar Sin a cikin gajeren lokaci.

 

 

Darakta janar na hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi tattaki zuwa kasar Sin, inda ya ganema idanunsa yadda shugaba Xi ke jagorantar ayyukan dakile annobar, har ya bayyana cewa, kasar Sin na daukar gagaruman matakai ba tare da wani jinkiri ba, abun da ba safai a kan ga irinsa ba a duniya. Kuma ya ce, tsarin kasar Sin mai karfi gami da managartan matakan da ta dauka, babban al'ajabi ne a duniya wanda ya cancanci yabo.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China