Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayoyin masanan WHO kan aikin yaki da cutar COVID 19 da Sin take gudanarwa
2020-02-25 21:55:23        cri
"An tabbatar da cewa, dabarar da Sin take aiwatarwa, ita ce hanya daya tilo da za a iya bi, wajen tinkarar cutar COVID 19. " Mai ba da shawara ga babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta WHO Bruce Aylward, shi ne ya yi wannan tsokaci a jiya Litinin.

An ce, a wannan rana, rukunin sa ido na masanan Sin da WHO kan cutar, ya kira wani taron manema labarai a nan birnin Beijing, inda aka bayyana cewa, matakin da Sin take dauka, ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, wanda ya haifar da ci gaba kwarai a fannin hana yaduwar cutar tsakanin al'umma, kana matakin ya tabbatar da cewa, mutane fiye da dubu 100 sun kaucewa, ko dakatar da kamuwa da cutar. Ban da wannan kuma, jami'in ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi sauran kasashe su sake kimanta matakan da suke dauka kan kasar Sin ba tare da bata lokaci ba.

Masana sun ba da wannan shawarar ne, bisa nazarin da suka yi a wuraren da cutar ta fi kamari. A cikin wadannan kwanaki 9, runkunin dake kunshe da masana daga kasashe 12, sun kai ziyara birnin Beijing, da lardin Guangdong, da Sichuan, da kuma Hubei da dai sauran wurare, bisa rakiyar masanan kasar Sin.

Yadda kasar Sin take gudanar da aikin yaki da kandagarkin cutar, da sakamakon da wadannan masana masu fada a ji suka gabatar, na iya samun amincewa daga bangarori daban-daban.

Saboda hadin gwiwar al'ummar Sinawa, da amfani da nagartattun manufofi, da bin doka da oda ba su gurgunta a kasar ta Sin ba, duk da cewa hakan kan auku, a lokacin da wata kasa take fuskantar babban bala'i ko annoba mai tsanani.

Ana ganin cewa, babban daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar a jiya Litinin cewa, lokacin da cutar ta fi kamari a kasar Sin ya wuce, kuma annobar ba ta yi mummunar yaduwa a duk fadin duniya ba.

A nasa tsokaci, shugaban kungiyar nazarin matakan yaki da kwayoyin cuta ta kasa da kasa, kana ferfesa mai nazarin kwayoyin cuta dakta Johan Neyts, ya bayyana cewa, Sin na daukar jerin ingantattun matakai masu amfani, wanda hakan ya baiwa sauran kasashen duniya isashen lokaci na tinkarar wannan mumunar annobar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China