Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa da kasa ba su amince da yunkurin da wasu 'yan siyasa suka yi na dorawa kasar Sin alhakin yaduwar cutar COVID-19 ba
2020-03-07 20:28:04        cri

Annobar cutar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya a halin yanzu, inda ake da wasu mutane dake yunkurin saka batun siyasa a ciki. Wasu masu kyamar kasar Sin daga kasashen yammacin duniya sun yi karyar cewa, rashin daukar kwararan matakan kandagarkin cutar da kasar ta yi ya sa kwayar cutar ta bazu zuwa sauran kasashe. Har ma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bata sunan kasar Sin, inda ya ce alkaluman kididdigar da kasar Sin ta bayar ba su cika ba, abun da ya kara wahalar da ayyukan dakile cutar a Amurka, a wani yunkuri na dorawa kasar Sin alhakin yaduwar cutar a Amurka.

 

 

Hakika, kasashen duniya suna ganewa idanunsu yadda kasar Sin ke nuna kwazo wajen tinkarar yaduwar cutar. Rahoton da tawagar hadin-gwiwar kwararrun masu binciken cutar COVID-19 na Sin da WHO ta fitar, ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki managartan matakan da suka dace don kandagarkin yaduwar cutar, al'amarin da ya taimakawa mutum akalla dubu 100 kaucewa daga kamuwa da wannan cuta. Kamar yadda ministar lafiyar kasar Masar ta ce, in ba don kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka ba tare da bata lokaci ba, duniya za ta kara fuskantar barazana.

 

 

Wasu 'yan siyasar kasashen yammacin duniya masu tsanar kasar Sin, ciki har da Mike Pompeo, na yunkurin dorawa kasar Sin laifi, da mayar da muradunsu ta fannin siyasa sama da muradun jama'a, don bata sunan kasar Sin gami da shafa mata bakin fenti, a yunkurinsu na wanke wasu 'yan kasashen yammacin duniya kalilan daga laifin rashin daukar kwararan matakan dakile yaduwar cutar ta COVID-19.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China