![]() |
|
2020-03-19 13:08:16 cri |
Kasashen da lamarin ya shafa sun hada da Sin, Italiya, Iran, Koriya ta kudu, Spaniya, Japan, Faransa, Jamus, Norway, Amurka, Birtaniya, Netherlands, da kasar Switzerland.
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya fadawa manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswar kasar wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranta, Aregbesola ya ce, matakin ya shafi dukkan kasashen da aka samu bullar cutar COVID-19 sama da guda 1,000 a kasar. Yace a halin da ake ciki yanzu an dakatar da bayar da biza kuma an soke dukkan bizar da aka riga aka baiwa 'yan kasashen ko kuma matafiya dake son yin bulaguro zuwa Najeriya daga kasashen.
Wannan mataki zai fara aiki ne tun daga ranar Asabar kuma za'a shafe tsawon makonni hudu ne, kana yanayin cigaban da aka samu shi ne zai nuna mataki na gaba da za'a dauka, in ji ministan.
Kawo yanzu kasar ta yammacin Afrika ta samu rahoton mutane 8 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China