Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zazzabin Lassa ya kashe mutane 161 a Najeriya
2020-03-19 10:46:12        cri
Hukumomin lafiya a Najeriya sun sanar cewa adadin mutanen da zazzabin Lassa ya kashe a kasar ya kai 161, ciki har da jami'an kiwon lafiya akalla hudu.

Chikwe Ihekweazu, babban daraktan cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC), ya ce, baki daya mutane 906 ne aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin kawo yanzu.

Ihekweazu ya fadawa manema labaru a Abuja cewa, yawan mutanen da ake zaton suna dauke da cutar ya karu matuka inda ya kai mutane 3,735.

Masana sun bayyana cewa ana iya yada zazzabin Lassa ta hanyar yawu, ko fitsari, ko kuma kashin bera wanda dan adam ya yi ta'ammali da shi. A wasu lokutan, Lassa yana kama da alamomin zazzabin maleriya.

Wata kididdigar masana yaduwar cutuka ta nuna cewa, galibi cutar zazzabin Lassa ta fi yaduwa a lokacin zafi tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China