Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 7 sun mutu sakamakon fadan kabilanci a Najeriya
2020-03-12 09:19:32        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane bakwai sun gamu da ajalinsu, sakamakon wani sabon fadan kabilanci da ya barke tsakanin al'ummomin Ngbo da Agila dake karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya.

Da yake Karin haske kan lamarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Ebonyi, Awosola Awotinde, ya bayyana cewa, an kuma lalata kadarori yayin fadan na ranar Talata. Su dai wadannan al'ummomi sun hada kan iyaka da Agila, wanda ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya. Wadannan al'ummomi dai, sun shafe gomman shekaru suna fada da juna, lamarin da har ya sanya hukumar shata kan iyaka ta Najeriya shiga tsakani.

Ko da yake jami'in karamar hukumar Clement Odah, ya bayyana cewa, fadan ya barke ne, lokacin da al'ummar Agila suka kai hari a kudu maso gabashin garin Ngbo a ranar Talata, inda suka rika harbin duk wanda suka gani.

Rundunar 'yan sandan jihar, ta ce ta kaddamar da farautar wadanda suka aikata kisan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China