Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta ce mutane miliyan 7.9 a arewa maso gabashin Najeriya suna bukatar tallafin jin kai a 2020
2020-03-05 10:20:29        cri

Ofishin kula da ayyukan jin kan bil adama na MDD (OCHA) ya tabbatar cewa, kimanin mutane miliyan 7.9 a shiyyar arewa maso gabashin MDD ta ce mutane miliyan 7.9 a arewa maso gabashin Najeriya suna bukatar tallafin jin kai a 2020  suna cikin yanayin bukatar agajin a shekarar 2020, kakakin MDD ya bayyana hakan.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDDr Antonio Guterres ya ce, sama da mutum guda cikin mutane biyu a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa suna cikin yanayin bukatar agajin.

Hukumomin samar da tallafin jin kan bil adama suna fuskantar karin matsaloli na rashin samun damar kaiwa yankunan da ake bukata, gami da matsaloli masu nasaba da tsaro wadanda ke haifar da koma baya ga ayyukan jin kan bil adama a jihohin uku, a cewar Dujarric, ya kara da cewa, sakamakon yawaitar hare haren da aka kaddamar a shekarar da ta gabata ya tilastawa hukumomin ba da agajin dakatar da ayyukansu da kuma janye wasu daga cikin jami'ansu na wucin gadi a wasu daga cikin yankunan.

Dujarric ya ce, MDD ta jaddada muhimmancin mutunta dokokin kasa da kasa da baiwa fararen hula kariya wadanda suka fada cikin tarkon rikici ba tare da son ransu ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China