Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta kafa kwamitin yaki da COVID-19
2020-03-18 19:26:28        cri
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin yaki da cutar COVID-19 da shugaban kasar ya kafa don tunkarar cutar.

Da yake karin haske yayin kaddamar da kwamitin a Abuja, babban birnin kasar, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Boss Mustapha ya bayyana cewa, matakan da gwamnatoci suka dauka a sassa daban-daban na duniya, ya nuna cewa, cutar COVID-19 ta haifar da babbar barazana ga daukacin bil-Adama, don haka wajibi ne kowace kasa ta dauki mataki, kimiya da dabaru gami da tsare-tsare.

Mustapha ya ce, mambobin kwamitin za su taimakawa kasar, a matakan da ta dauka a sassa da wanda gwamnatoci ke dauka kan yaki da cutar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China