Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labarai ta Najeriya ta zargi wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma da murguda gaskiya kan kasar Sin
2020-03-06 10:14:38        cri

Jaridar Peoples Daily da ake wallafawa a tarayyar Najeriya, ta wallafa wani bayanin da wani masani dan kasar Pakistan Yasir Masood ya rubuta, mai taken "Gaskiya da kuma karairayi game da cutar COVID-19", inda ya zargi kafofin yada labarai na kasashen yamma, masu fakewa da sunan "'yancin fadin albarkacin baki" don mai da kalubalen cutar, a matsala wani makamin siyasa. Bayanin ya kuma yi kira ga daukacin Bil Adama na kasa da kasa, da su shiga yaki da cutar cikin hadin kai.

Bayanai na nuna cewa, wannan cuta kamar sauran bala'u daga indallahi, ba su da iyakar kasa ko al'umma, wato dai cuta ce dake kiyayya ga daukacin Bil Adama.

Yayin da ake namijin kokarin yaki da wannan mumunar cutar, kafofin yada labarai na kasashen yamma, ciki hadda jaridar "The Wall Street" ta kasar Amurka ta fake bisa hujjar "'yancin fadin albarkacin baki", don shafawa kasar Sin bakin fenti ba gaira ba dalili, ta yadda za su cimma burinsu na illata bunkasuwar kasar Sin.

Irin wannan mataki na rashin imani da suke dauka, na neman cimma manufar siyasa, sun keta moriyar Bil Adama, kuma ba komai cikin su sai munafunci a zukatunsu, ta yadda al'umomi daban-daban ke watsi da su.

Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, Sin ta koyi fasaha matuka daga cutar SARS, wadda ta barke a shekarar 2003, an kuma yi imanin cewa, za a kawo kashen wannan cutar da ake fuskanta yanzu ba da bata lokaci ba. A halin yanzu kuma, al'ummar duniya kamata ya yi ta yi hadin kai, don goyon bayan jaruman da suke yaki da cutar a fagen daga, duba da cewa, baya ga kokarin kiyaye kasar Sin, suna kuma bautawa dukkanin Bil Adama baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China