Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko 'Yan Siyasar Amurka Za Su Iya Boye Laifinsu?
2020-03-17 20:51:05        cri

Jiya Litinin, manyan jami'an harkokin wajen kasashen Sin da Amurka suka zanta ta wayar tarho.

Cikin zantawar tasu, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyar Kwaminis ta kasar Sin, JKS, kana darektan kula da harkokin diflomasiyya na kwamitin kolin, Yang Jiechi ya bayyana wa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo cewa, wasu 'yan siyasar kasar Amurka na ci gaba da kokarin bata sunan kasar Sin da kuma musanta matakan kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta dauka, kuma hakan ya bata ran al'ummomin kasar Sin. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasar Amurka ta gaggauta gyara kuskurenta, ta kuma daina zargi maras tushe da take yi wa kasar Sin.

Hakika dole ne a fahimci bacin ran kasar Sin. A cikin wata guda da ya gabata, al'ummomin Sin sun sadaukar da kai wajen dakile yaduwar cutar COVID-19, kuma kokarin da kasar Sin ta yi na kandagrki da hana yaduwar cutar, ya samu yabo daga gamayyar kasa da kasa. Amma, a maimakon mai da hankali kan hana yaduwar cutar, wasu 'yan siyasa na kasar Amurka sun fi mai da hankali kan rura wutar nuna wariyar launin fata, da zargi tsarin siyasar kasar Sin, domin bata sunan kasar Sin cewar, wai Sin ce ta kirkiro wannan cuta.

Haka zalika, Mike Pompeo ya sha kiran cutar numfashi ta COVID-19 da "cutar Wuhan", sannan Donald Trump, shugaban kasar Amurka ya kira wannan cuta da "cutar Sin", lamarin da ya bata ran kasashen duniya. Irin wannan abin da suka yi rashin hankali ne, kana ya saba ka'idar kimiyya da fasaha, da ka'idar hukumar WHO na rashin dacewar sanyawa wata cuta sunan wata kasa ko wani yanki.

Yanzu, babban aikin dake gaban kasa da kasa shi ne hada kai wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, amma kasar Amurka tana son boye laifinta, har tana son biyan wani kamfanin hada magunguna na kasar Jamus dallar Amurka biliyan daya don ya samar mata allurar rigakafin cutar ita kadai, lamarin da ya bata hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da cutar, inda aka siyasantar da kwayar cutar, wadda ya kamata mu kawar da ita.

Sa'an nan, a ranar 16 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas ya sanar da cewa, kasar Jamus ba za ta sayar da 'yancinta na nazarin allurar rigakafi ba. Kuma babbar jaridar Bonn ta kasar Jamus ta wallafa wani sharhi dake cewa, lalle kasar Amurka ta nunawa duniya mugun halinta.

Yang, ya bukaci wasu 'yan siyasa na kasar Amurka su mai da hankali kan shawarar da kasar Sin ta gabatar musu cewa, bai dace su raina aniyar kasar Sin na kare martaba da mudarunta ba. Daga ina wannan cuta ta fito, bincken kimiya ne kadai zai ba ta wannan amsa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China