Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka suna kiyaye yin kokari don neman cimma yarjejeniya a tsakaninsu
2019-10-27 16:15:21        cri
Masu jagorancin shawarwari game da tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka sun buga wayar tarho ga juna a ranar 25 ga wata, inda suka amince da daidaita batutuwan da suka sanya a gaba, da tabbatar da kammala wasu abubuwa a fannin fasahohi ta hanyar shawarwarin, kana sun cimma daidaito kan wasu ayyukan da za a gudanar. Wannan ya shaida cewa, bangarorin biyu suna kokarin daidaita matsaloli a fannin fasahohi, da sa kaimi ga cimma burinsu, da kuma aza tubali wajen daddale yarjejeniya a tsakaninsu a wannan mataki.

Ana ganin cewa, ana bukatar lura da batutuwan dake shafar moriyar bangarorin biyu bisa tushen adalci da girmamawar juna don cimma yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka. Sin tana gudanar da ayyukan daidaita batutuwan da Amurka ke kulawa kamar sayen kayayyakin noma, da sarrafa Fentanyl da sauransu, kana Sin tana kula da batutuwa uku wato soke dukkan harajin kwastam da aka kara mata, da kididdigar saya da sayarwa ta dace da hakikanin yanayi, da a tabbatar da adalci a kan rubuce-rubucen da bangarorin biyu suka tattauna.

An jaddada cewa, ya kamata a daidaita matsaloli bisa tushen girmamawa juna, da fadada hadin gwiwa bisa tushen samun moriyar juna, saidai Sin da Amurka su ci gaba da yin kokari, watakila za a cimma yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya dake amfanawa bangarorin biyu har ma ga dukkan duniya baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China