Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ba za ta iya boye ainihin mugun nufinta ba
2019-11-28 20:20:50        cri

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya rubuta wani sharhi yau cewa, duk da adawar da kasar Sin ta nuna, amma sai da kasar Amurka ta zartas da doka kan hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Wannan ya nuna cewa, ba za ta iya boye ainihin mugun nufinta ba.

Wasu Amurkawa sun yi wa 'yan siyasansu ba'a a shafin intanet cewa, suna wuce makadi da rawa, ba su iya tafiyar da harkokin kasarsu yadda ya kamata ba, balle ma sa tsoma baki a kan Hong Kong. Wasu kuma sun zargi shugabannin kasar da cewa, Hong Kong, ba yankin Amurka ba ne, yanki ne na kasar Sin. Bai kamata ba a sa tsoma baki a harkokin wata kasa ba.

Sharhin ya jaddada cewa, Hong Kong, yankin musamman ne na kasar Sin. Gwamnatin tsakiyar kasar Sin da mahukuntan Hong Kong su ne kawai suke da ikon tafiyar da harkokin yankin. Wasu 'yan siyasan Amurka sun yi ta tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasar Sin da sunan "neman dimokuradiyya da 'yanci ga al'ummar yankin". Wannan ba komai ba ne, ila neman rura wutar tarzoma a Hong Kong, hana ci gaban kasar Sin da yin juyin mulki a kasar Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China