Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Shirin doka kan HK tamkar wasan yara ne
2019-11-28 20:19:39        cri

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya rubuta wani sharhi yau cewa, kasar Amurka ta zartas da doka kan hakkin Bil Adama da dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a ranar 27 ga wata, wannan tsoma baki ne a harkokin Hong Kong da kuma harkokin cikin gida na kasar Sin. Wannan tamkar wasan yara ne, wanda kasar Sin da kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi da babbar murya.

Harkokin yankin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Abin da Amurka ta yi ya saba wa dokokin duniya da manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Amurka ta zartas da doka kan Hong Kong da sunan "kiyaye hakkin dan Adam", wannan ya nuna cewa, tana goyon bayan masu tarzoma a fili. Ta kuma lalata moriyar al'ummomin Hong Kong. Ya zama tilas a kwantar da kura da dawo da doka da oda a yankin cikin hanzari.

Sharhin ya jaddada cewa, Amurka na yunkurin hana ci gaban kasar Sin ta hanyar tsoma baki a cikin harkokin Hong Kong. Tana zaton gwamnatin Sin ba za ta iya daidaita barazanar yadda ya kamata ba. Babu wata kasa ta ketare da za ta sa kasar Sin ta yi watsi da muhimman muradunta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China