Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Tabbas wadanda suka yi yunkurin rura wutar tarzoma a wata kasa za su sha wahala
2019-11-25 21:04:09        cri

Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a shekarar 2019, inda ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, a fili yake cewa, ta goyi bayan masu tada kayar-baya wadanda ke da tsattsauran ra'ayi. Wasu 'yan siyasan Amurka sun yi yunkurin sake rurar wutar tarzoma a wata kasa, sun dade suna yin danniya da bin siyasar nuna fin karfi, lamarin da ya bata rayukan kasashen duniya sosai.

Wasu 'yan siyasan Amurka suna goyon bayan ta da tarzoma, hakan ya saba wa dokokin duniya da muhimman ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, ba kawai hakan ya bata sunanta ba, har ma zai ba su kansu wahala.

Yankin Hong Kong, yanki ne na kasar Sin. Kasar Sin na tsayawa kan kiyaye ikon mulkin kasa, tsaron kasa da ci gabanta. Ba ta sauya aniyarta ta bin manufar "aiwatar da tsarin mulkin biyu a cikin kasa daya" ba. Ba ta sauya aniyarta ta kin yarda da a sa hannu cikin harkokin Hong Kong ba. Dukkan abubuwan da aka yi domin hana ci gaban kasar Sin ta hanyar rura wutar tarzoma ba za su yi nasara ba, kana kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China