Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa ba za su ja da baya sakamakon barazanar wasu ba
2019-11-29 20:16:55        cri
Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya rubuta wani sharhi yau cewa, yayin da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gaggauta kwantar da kura da dawo da doka da oda, kasar Amurka ta zartas da doka kan hakkin dan Adam da dimokuradiyya a yankin a kwanan baya, a yunkurin bai wa 'yan daba masu tsattsauran ra'ayi na Hong Kong damar tserewa, illata kwanciyar hankali da wadata a yankin, kawo cikas wajen aiwatar da "tsarin mulki biyu a kasa daya" yadda ya kamata, da dakatar da farfado da al'ummar Sinawa. Jama'ar Sin ba za su yarda da haka ba.

Sharhin ya ce, a baya Amurka ta sha tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, ta hada kai da wadanda suke adawa da kasar Sin da kuma haddasa barna a Hong Kong, a yunkurin samun riba sakamakon ta da tarzoma a yankin. Abubuwan kunya da Amurka ta yi sun nuna cewa, Amurka tana goyon bayan yin barna a Hong Kong a asirce. Mugun nufinta shi ne yin amfani da damar haddasa barna a Hong Kong don hana ci gaban kasar Sin.

Sharhin ya jaddada cewa, tun can har kuma zuwa yanzu jama'ar Sin ba su ja da baya sakamakon matsin lamba ba. Abun da Amurka ta yi ya sanya daukacin Sinawa kara fahimtar mugun nufin Amurka da kuma danniyar da take yi. Jama'ar Sin za su kara hada kai da nuna karfin hali wajen daidaita barazanar da wasu ke musu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China