Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kwantar da kura a Hong Kong, shi ne abin da al'ummomin yankin ke bukata
2019-11-26 20:40:53        cri

Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a shekarar 2019, lamarin da ya tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin da goyon bayan masu tada kayar-baya a fili. Kasar Sin ta ki amincewa da kuma yin tir da abin da Amurka ta yi. Yanzu haka abubuwan da suke faruwa a Hong Kong ba su da nasaba da batun kiyaye hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya. Ya zama tilas a kawo karshen hankalin dake faruwa da dawo da doka da oda da tabbatar da aiwatar da doka cikin hanzari. Abin da Amurka ta yi ba tare da jin kunya ba ya saba wa doka, ya kuma yi saba da bukatun al'umma. Don haka, ba za ta yi nasara ba.

Yanzu al'ummomin yankin Hong Kong masu adalci suna daukar matakan da suka kamata da kuma mayar da martina mai karfi. An shawarci wasu Amurkawa da su hanzarta daina goyon bayan aikace-aikacen nuna karfin tuwo, su daina fakewa da sunan Hong Kong suna tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. In ba haka ba, kasar Sin za ta mayar da martini mai karfi. Duk yunkurin da ake yi na neman sanya Hong Kong cikin rashin kwanciyar hankali zai ci tura! Munafuncin dodo ya kan ci mai shi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China