Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna da takwaransa na Pakistan
2020-03-17 20:32:29        cri
A yau Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Pakistan Arif-ur Rehman Alvi dake ziyara a nan birnin Beijing,fadar mulkin kasar Sin.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin yanzu cutar COVID-19 ta bullo a sassa daban-daban na duniya. Don haka, a shirye kasar take ta kara ba da gudummawa wajen hana yaduwar wannan cuta a duniya, kana za ta ci gaba da baiwa Pakistan goyon baya da taimako.

A nasa jawabin Alvi, ya bayyana cewa, JKS da gwamnatin kasar Sin, sun nuna shugabanci na gari wajen tunkarar wannan annoba. Haka kuma, fasahohi da matakan kasar Sin, sun samar da kyawawan darussan ga sauran kasashe. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China