Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya ziyarci asibitin Huoshenshan
2020-03-10 13:53:13        cri

Bayan isowarsa Wuhan da safiyar yau Talata, shugaba Xi Jinping ya yi tattaki zuwa asibitin Huoshenshan, wato asibitin wucin gadi da aka gina domin kulawa da masu kamu da cutar numfashi ta COVID-19, don ganewa idanunsa yadda ake tafiyar da harkokin asibitin, da baiwa masu kamu da cutar magani, da samar da kariya ga ma'aikatan jinya, da kuma binciken kwayar cutar da sauransu.

Shugaba Xi ya kuma mika gaisuwa ga wadanda ke karbar magani a asibitin, da jinjinawa ma'aikatan jinyar da suke aiki ba dare ba rana, don karfafa musu gwiwar samun galaba kan aikin ganin bayan cutar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China