Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya amsa wasikar matasan likitocin dake yaki da COVID-19 a Hubei
2020-03-16 13:46:05        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa matasan likitocin dake aikin yaki da COVID-19 gwiwar bayar da gudunmuwarsu a wuraren da JKS da jama'a suka fi bukata.

Shugaba Xi Jinping, wanda shi ne sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake amsa wasikar da wasu matasa likitoci 34 suka aike masa. Matasan mambobin JKS ne dake cikin tawagar likitocin da jami'ar Peking ta tura domin su taimaka wajen yaki da cutar COVID-19 a lardin Hubei, wato inda cutar ta samo asali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China