Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jinjinawa ma'aikatan jinya a Wuhan
2020-03-10 20:41:17        cri
A lokaci mai muhimmanci na dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin aikin soja na kasar Xi Jinping ya ziyarci birnin Wuhan na lardin Hubei, domin rangadin aikin dakile annobar.

A cibiyar ba da umurni ta asibitin Huoshenshan, Xi ya tambayi wakilan ma'aikatan jinya dake aiki ta wayar tarho yanayin da suke ciki, inda ya ce, "Dukkanku kuna sanya kayan kariya, da kayan rufe baki da hanci, ba na iya ganin fuskokinku, amma a zuciyata, dukkanku mutane ne mafi kwarjini, a nan ina gaishe ku, da girmamawa gare ku, a madadin kwamitin tsakiya da JKS. "

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China