Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping Ya Nemi A Nuna Babban Goyon Bayan Kimiyya Da Fasaha Domin Cimma Nasarar Shawo Kan Cutar COVID-19
2020-03-15 21:07:04        cri

A ranar 16 ga wata, Majallar Qstheory ta kasar Sin za ta wallafa wani muhimmin bayani mai taken "Nuna babban goyon bayan kimiyya da fasaha domin cimma nasarar shawo kan cutar numfashi ta COVID-19" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta.

A cikin bayanin, shugaba Xi ya jaddada cewa, makami mafi karfi da bil Adama za su iya yin amfani da shi wajen yaki da cututtuka shi ne kimiyya da fasaha, ba za mu iya cimma nasara ba idan babu ci gaban kimiyya da fasaha da bunkasuwar fasahohi. Ya kamata mu mai da aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ta hanyoyin kimiyya da fasaha a matsayin muhimmin aiki dake gabanmu, yayin da warware matsalolin da ake fuskanta wajen dakile yaduwar cutar cikin sauri ta hanyar hada ilmin fannoni daban daban, domin nuna babban goyon baya na kimiyya da fasaha ga al'umma wajen yaki da cutar.

Haka kuma, ya ce, ya kamata mu hada ayyukan dake shafar magani da sarrafa na'urorin jinya da ba da jinya ga mutane tare, domin samun karin mutanen da za su warke daga cutar da rage adadin mutanen da za su rasu a sakamakon cutar. Kuma aiki mafi muhimmanci dake gabanmu shi ne ceto mutane. Sa'an nan kuma, mu gaggauta ayyukan nazarin a yi rigakafi da kuma tsara aikin yin kandagarki yadda ya kamata, wanda mai iyuwa ne zai zama aiki na yau da kullum.

Ya kara da cewa, ya dace mu daidaita aikin gano asalin cutar da hanyoyin yaduwar cutar, da maida hankali kan halin da wadanda suka warke daga cutar, da ma wadanda aka killace su a gida. A sa'i daya kuma, mu kyautata tsarin kandagarki kan cututtuka da aikin kiwon lafiyar al'umma. Saboda cututtuka masu yaduwa da kalubalen dake shafar halittu dukkansu suna shafar tsaro da ci gaba na wata kasa, da ma zaman karko na zamantakewar al'umma. Ya kamata mu maida tsaron halittu daya daga cikin manyan batutuwan dake shafar tsaron kasa.

Cikin bayanin, shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, ya kamata mu fara aikin kiwon lafiya don nuna kishin kasa. Mu shimfida wannan aiki daga fannonin kyautata muhalli, al'adar cin abinci, na'urorin kiwon lafiya na jama'a da sauransu, musamman ma, daina cin naman daji, da kuma sa kaimi ga al'umma da su yi zaman rayuwa cikin lafiya da kare muhalli.

Bugu da kari, ya ce, ya kamata mu karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa kan kimiyya da fasahar yin kandagarkin cutar. Kiwon lafiyar al'umma shi ne babban aikin dake gaban dukkanin bil Adama, yana bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, domin samar da karfi da ilmi wajen inganta dunkulewar kasa da kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China