Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tabbatar da cimma nasara a yaki da cutar COVID-19 a Wuhan
2020-03-10 21:04:10        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, Sin za ta cimma nasarar yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19. Shugaban ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin ziyarar gani da ido da ya kai birnin Wuhan, fadar mulkin lardin Hubei.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya yi kira da a kara kwazo, da himma cikin kyakkyawan tsarin kandagarki, da shawo kan cutar a lardin Hubei da ma birnin Wuhan baki daya.

Xi ya ce bayan gudanar da aiki tukuru, yanayin da ake ciki a lardin Hubei da birnin Wuhan ya kara kyautata, an kuma samu ci gaba, to sai dai kuma matakan kandagarki da shawo kan cutar, aiki ne mai matukar wahala.

Daga nan sai ya jaddada kudurin Sin, na ci gaba da yaki da wannan annoba a matakai na kandagarki da shawo kan ta, a matsayin aiki mafi muhimmanci.

A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tabbatar da cewa, matakai masu nagarta da ake dauka na kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, sun haifar da nasara ne sakamakon sadaukarwa, da jajircewa, da juriya da aiki tukuru na al'ummar Wuhan, birnin da cutar ta fara bulla.

Ya ce dagewar su wajen aiki, ya sa al'ummar Wuhan bayyana karfin himmar Sin, da ma irin yadda Sinawa ke son iyalan su da kuma kasar su, matakin da ya sa suke iya kaiwa ga nasara a halin wuya ko dadi.

Shugaban na Sin ya mika sakon ta'aziyyar sa bisa al'ummar Sinawa da wannan cuta ta COVID-19 ta hallaka, da jinjina ga wadanda suka sadaukar da rayukan su wajen yaki da annobar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China