Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yanci da rayuwa, wane ya fi muhimmanci?
2020-03-17 19:47:00        cri

A ranar 13 ga wata, a zantawarsa da wakilin New York Times Donald McNeil Jr., mai gabatar da shirin talabijin na kamfanin dillancin labarai na NBC na kasar Amurka ya bayyana cewa, yadda kasar Sin take yaki da cutar numfashi ta COVID-19 bai mai da hankali kan kare 'yancin al'umma kamar yadda kasashen yammacin duniya suke yi ba.

Dangane da wannan batu, Donald McNeil Jr. ya bayyana cewa, abubuwan dake da matukar daraja su ne 'yancin rayuwa, walwala da kasancewa cikin farin ciki, amma, idan babu 'yancin rayuwa, babu abin da za ka iya yi da sauran biyu. Ya ce, bayanin da hukumar WHO ta yi kan babban burin kasar Sin wajen yaki da cutar shi ne ceton mutane, ko da yake wannan zai haifar da cikas ne na gajeren lokaci ga rayuwar jama'a. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China