Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Sama da mutane 4,000 sun mutu sakamakon annobar cutar COVID-19 a duk fadin duniya
2020-03-11 10:38:25        cri
Sabbin mutane 203 ne suka mutu a sanadiyyar annobar cutar numfashi ta COVID-19 cikin sa'o'i 24 da suka gabata a fadin duniya ya zuwa safiyar ranar Talata, inda kawo yanzu yawan wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar a fadin duniya ya kai 4,012, a cewar rahoton hukumar lafiya ta duniya (WHO) wanda ta fitar a safiyar ranar Talata.

Baki daya mutane 113,702 aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a fadin duniya ya zuwa ranar Talata, inda aka samu karin sabbin mutane 4,125 da suka kamu da cutar daga cikin yawan adadin na baya. Daga cikin adadin, sabbin mutane 4,105 da suka kamu da cutar daga wajen kasar Sin ne.

Kasashen Brunei, Mongolia, Cyprus, Guernsey da Panama an samu rahoton bullar cutar ta COVID-19 a karon farko, hakan shi ya kawo yawan kasashe da yankuna na duniya da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 zuwa 109.

Haka zalika, hukumar WHO ta yi nazari game da nau'ikan hanyoyin yaduwar cutar a kasar Macedonia ta Arewa, Poland, Pakistan a matsayin kasashen da aka samu yaduwar cutar ta hanyar shigo da cutar daga waje kadai zuwa hanyar yaduwar cutar a cikin gida, hakan ya sa yawan kasashe da yankunan duniya da aka samu yaduwar cutar a cikin gida zuwa 61 da kuma kasar Sin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China