Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID-19 ba ta kai ga zama annobar gama-duniya ba
2020-03-06 10:16:31        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ya zuwa yanzu, ba za a iya ayyana cutar numfashi ta COVID-19 a matsayin cutar gama-duniya mai tsanani ba tukuna, duk kuwa da cewa tana ci gaba da shiga wasu karin kasashen duniya da a baya babu.

Mr. Adhanom wanda ke tsokaci yayin taron manema labarai na rana rana da ya gudana a jiya Alhamis, ya ce abu mafi tada hankali shi ne, yadda cutar ke kara shiga karin kasashe, ciki hadda masu raunin tsarin kula da lafiya, inda kuma za ta iya yin ta'adi mai yawa.

To sai dai kuma a daya bangaren, jami'in ya ce tasirin cutar na iya dara wanda ake gani a yanzu, duk da dai akwai wasu alamu da suke nuna za a iya shawo kan ta. Ya ce yaki da cutar gwagwarmaya ce da ba za a tsagaita ta ba, har sai an ga bayan cutar baki daya.

Ya zuwa safiyar jiya Alhamis, adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya baki daya ya kai mutum 95,265, ciki hadda mutane 3,281 da cutar ta hallaka. Amma duk da haka, Mr. Tedros ya ce ana iya ayyana cutar COVIC-19 a matsayin cutar gama-duniya ne kadai, idan dukkanin alkaluma suka tabbatar da haka, amma yanzu dai lokaci bai yi ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China